An soke dakatar da aka yi wa dan wasan Brazil Barbosa

Gabriel Barbosa zai ci gaba da buga wa Flamengo wasannin, bayan da kotun daukaka kararrakin wasanni ta wanke shi.

An yanke masa hukuncin dakatar da dan kwallon Brazil shekara biyu kan zargin shan abubuwan kara kuzarin wasa

Wanda aka fi sani da Gabidol, mai shekara 27, an dakatar da shi a cikin watan Maris, bayan da ya yi kokarin lalata gwajin shan abubuwan kara kuzarin ‘yan wasa da aka yi masa.

An zargi dan wasan da cewar tun a ranar farko da za a yi masa gwajin a Brazil, abokan tamaularsa sun je an yi musu da safe, shi kuma bai je ba da yammaci ba.

Ranar da ya amince ya je gwajin sai ya tashi hankalinsa da yin hayaniya, saboda wani jami’in da zai yi gwajin ya bi shi bandaki.

Gabiyol fitatce daga ‘yan wasan Flamingo da suka lashe lik a 2019 da Copa Libertadores ya musanta cewar ya yi kokarin kwange wajen bayar da samfurinsa.

Wanda ya taka leda a Santos tun daga makarantar horar da tamaula, bai taka rawar da ta dace a Benfica da Inter Milan ba, daga nan ya koma Flamengo a 2019.

Ya koma kan ganiya a Flamengo da ta kai tawagar Brazil ta mika masa goron gayyata, wadda ya yi wa wasa na 18 cikin janairun 2022.

Kwantiragin Gabigol da Flamengo zai kare a cikin watan Disambar 2024.

Leave a comment