An sayar da rigar Messi shida kan $7.8 million

Rigar da Lionel Messi ya saka a gasar kofin duniya a Qatar a 2022, guda shida an sayar da su $7.8 million.

A wajen da aka gudanar da gwanjon rigunar an yi tayi biyu tun farko daga baya aka sallama na uku a rigar da Argentina ta saka mai launin ruwan bula da layi mai ratsin fari.

Wannan shi ne ciniki mafi tsoka da aka yi a fannin kayayyakin wasa a duniya a shekarar nan.

Messi ya ja ragamar Argentina zuwa wasan karshe da ta doke France da ci 4-2 a bugun fenariti ranar 18 ga watan Disamba a filin wasa na Lusail, mai cin ‘yan kallo 80,000.

Kofin duniya na farko da Argentina ta dauka tun bayan Diego Maradona, kuma na uku jimilla.

A farkon watan nan Time Magazine ta bayyana Messi a matakin fitatcen dan wasa na 2023.

Messi, wanda ya koma taka leda a gasar kwallon kafar Amurka, MLS shi ne ya lashe kyautar Ballon d’Or na 2023 kuma na takwas jimilla.

Mai shekara 36 ya fara bugawa sabuwar kungiyarsa Inter Miami wasa a cikin watan Yuli, bayan da ya koma can da taka leda daga Paris Saint-Germain.

Ya taka rawar da Inter Miami ta lashe League Cup, wanda shi ne na farko da ta dauka a tarihi.

Tun kafin yarjejeniyar kyaftin din Argentina ta kare a PSG, kungiyoyi da dama a gasar Saudi Arabia sun yi zawarcin tsohon dan wasan Barcelona, wanda daga baya ya zabi zuwa Amurka.

Leave a comment