An sake zabar Tebas shugaban gudanar da LaLiga

An kara zabar Javier Tebas a matakin shugaban gudanar da gasar La Liga ta Spain zango na hudu.

Tebas, mai shekara 61 ya yi ritaya daga aikin a cikin watan Satumba, domin yin takara karo na hudu kuma shi kadai ne dan takara.

Ya fara aikin shugaban gasar LaLiga a karon farko a Afirilun 2013 aka sake zabarsa a 2016 da kuma 2019.

Tebas tsohon shugaban Huesca na shan yabo kan yadda ya bunkasa gasar LaLiga da samar da yarjejeniyar nuna wasannin a talabijin, bayan da a baya aka dogara da kungiyoyi su tattauna da masu son nuna wasanninsu.

Ya goga da shugaban Real Madrid da na Barcelona, wadanda suka yi shirin kirkirar gasar da za ta amfane su mai suna, European Super League amma shirin bai yi tasiri ba.

Ya kuma sha caccakar masu Manchester City da Paris St Germain cewar suna karya dokar kasha kudi daidai samu ta hukumar Turai.

Leave a comment