An kawo karshen wasa14 a jere ba a doke Argentina ba

Uruguay ta je ta ci Argentina 2-0 a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a 2026.

Darwin Nunez da ke taka leda a Liverpool shi ne ya ci kwallo na biyu, bayan da Ronald Araujo ya fara zura na farko.

Rabon da Argentina ta yi rashin nasara tun bayan da Saudi Arabia ta do ke ta 2-1 a gasar kofin duniya a Qatar.

Kenan an kawo karshen wasa 14 da ta buga a jere ba tare da an yi nasara ba a kan Argentina.

Karon farko da Messi bai ciwa kasarsa kwallo ba, tun daga wanda bai yi ba a karawa da Poland a Qatar a wasan cikin rukuni a gasar kofin duniya.

Kwallon da Araujo ya ci Argentina karon farko kenan tun bayan wadanda Faransa ta zazzaga mata a Qatar.

Hukumar kwallon kafa ta Uruguay ta nada tsohon kociyan Leeds United, Marcelo Bielso tun daga watan Mayu, domin ya kai kasar gasar kofin duniya a 2026.

Argentina wadda ta ci wasa da fara wasannin Kudancin Amurka da rashin nasara daya har yanzu tana kan teburi da maki 12.

Uruguay kuwa mai maki 10 tana ta biyu, bayan wasa biyar-biyar.

Amurka da Canada da Mexico ne za su karbi bakuncin gasar kofin duniya da za a yi a 2026.

Leave a comment