An kashe mai gudun fanfali Kiplagat da wuka a Kenya

An kashe dan gudun fanfalaki, Benjamin Kiplagat a Kenya, kamar yadda ‘yansanda suka ce an daba masa wuka ne.

Dan kasar Uganda, wanda aka haifa a Kenya, mai shekara 34 ya wakilci Uganda a gudun mita 3,000 da wasannin Olympic da gasar tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya.

An samu gawarsa a cikin wata mota a Rift Valley a Eldoret, garin da ‘yan wasa da dama ke atisaye.

Kiplagat, wanda ya yi shekara 18 yana wasannin guje-guje ya lashe zinare a gudun mita 3,000 a gasar duniya ta matasa a 2008 da tagulla a gasar Afirka a 2012.

Ya kai wasan daf da karshe a Olympics a 2012 da aka yi a London, ya kuma halarcin gasar da aka yi a Rio a 2016.

A Oktoban 2021, aka kashe Agnes Tirop, wadda aka dabawa wuka a gidan da take.

Mai shekara 25 ta wakilci Kenya a wasannin guje-guje da yawa.

Leave a comment