An kara cire wa Everton maki biyu bayan karya dokar Premier

An kara kwashe maki biyu a Everton sakamakon karo na biyu da aka samu kungiyar da laifin karya dokar faduwa kasuwanci a Premier League.

An amince kungiya ta fadi kasuwancin £105m cikin kaka uku, yayin da kwamiti mai zaman kansa ya samu Everton da faduwa kasuwacin sama da £16.6m kan kudin da aka gindaya a shekara uku zuwa kakar 2022-23.

Hakan ya sa kungiyar ta yi kasa zuwa ta 16 a kasan teburi da tazarar maki biyu tsakaninta da ‘yan ukun karshe.

Tun farko an kwashe maki 10 daga Everton a bana daga baya ya koma shida, bayan daukaka kara cikin watan Fabrairu kan kasuwancin da ta gudanar na shekara uku zuwa kakar 2021-22.

Kungiyar ta Everton ta sanar da cewar za ta kara daukaka kara, kamar yadda ta yi a hukuncin farko.

Watakila a kara kwashe wa kungiyar Merseyside maki, sakamakon kudin ruwa da ya shafi gina sabon filin wasa a Bramley-Moore Dock, koda yake ana sa ran kungiyar za ta shawo kan matasalar kafin karshen kakar nan.

Leave a comment