An fitar da Ramadan Garba daga damben gwamnan jihar Kano

An fitar da Ramadan Garba daga gasar damben Gwamnan Jihar Kano bayan rashin nasara da ya yi a hannun Lawi ɗan Hadejia a ranar Talata a filin wasa na Ado Bayero Square, Kano, Najeriya.

Lawi ɗan Hadejia ne ya samu nasara a fafatawar da suka yi a turmi uku, inda Ramadan Garba ya sha wahala da kasa kai dambe, tare da yawan fita daga layi fiye da ka’ida.

Wani abin da ya ja hankalin masu kallo shi ne rashin iya kai naushi mai ƙarfi daga Ramadan, yayin da abokin hamayyarsa ya fi nuna kokari da ƙwazo a wasan.

Rahotanni sun bayyana cewa Ramadan Garba ya dade yana fama da raunin hannun dama, wanda hakan ya iya shafar yadda ya taka rawa a wannan fafatawa. Duk da haka, ya yi shiri sosai a watan azumi domin dawowa cikin tsari kafin gasar damben gwamna ta fara.

Yanzu haka, Ramadan Garba yana da damar komawa gasar damben Sarauta da za a yi a lokacin Babbar Sallah, inda manyan ’yan dambe za su fafata domin neman kambun Sarkin Damben Kano.

A halin yanzu, Ali Kanin Bello shi ne ke rike da sarautar damben Kano, bayan da ya doke Dogo Mai Takwasara a Ado Bayero Square.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top