An fitar da kungiyoyin England daga Champions da Europa League

An yi waje da dukkan kungiyoyin Premier League daga Champions da Europa League na bana a zagayen quarter finals.

An fitar da Liverpool a Italiya duk da cin 1-0 da ta yi a gidan Atalanta a gasar zakarun Turai ta Europa ranar Alhamis.

An doke Liverpool da ci 3-1 gida da waje, bayan da Atalanta ta yi nasarar dura 3-0 a Anfield a makon jiya.

West Ham United ma an yi waje road da ita, bayan da ta tashi 1-1 da Bayern Leverkusen, mai Bundesliga a bana na farko a Tarihi.

An ci kungiyar David Moyes 2-0 a wasan farko a daf da na kusa da na karshe a Jamus a makon jiya.

Sau uku kenan a karni na 21 da ata fitar da ba kungiya daga Ingila a zagayen daf da karshe a Champions da Europa League.

Kuma karo na hudu daga kaka 20 da ba za a samu kungiyar dake buga Premier League ba a wasan karshe a gasar ta zakarun Turai mai daraja ta daya da ta biyu.

Sauran sakamakon wasannin, Roma ta kai bantenta da cin 3-1, gida da waje, bayan da ta yi nasara a kan AC Milan 2-1 a jiya – tun farko ta zura 1-0 a San Siro. Olympic Marseille ce ta kai zagayen gaba a kan Benfica ta Portugal.

A ranar Laraba Real Madrid ta fitar da Manchester City a bugun fenariti a Champions League, bayan da suka tashi 1-1 a Etihad – tun farko sun buga 3-3 a Spaniya.

Arsenal ma ta yi ban kwana da gasar zakarun Turai ta bana da rashin nasara a gidan Bayern Munich da ci 1-0, wadda ta kai zagayen gaba da kwallo 3-1, bayan da suka yi 2-2 a Emirates a makon jiya.

Har yanzu Arsenal ba ta taba lashe Champions League ba, karo na biyar da Bayern ke fitar da ita a zagayen karawa gida da waje.

Za a buga daf da karshe tsakanin Olympique Marseille da Atalanta da na Roma da Bayer Leverkusen.

Za a fara karawa ranar 2 ga watan Mayu, wasa na biyu ranar 7 ga watan gobe.

Leave a comment