An fara damben gwamnan jihar Kano ranar karamar Sallah

Filin wasa na Ado Bayero Square a Kano a Nigeria ya karbi ‘yan kallo makil ranar karamar Salah da aka fara damben gwamnan jihar Kano, Engineer Abba Kabir Yusuf.

An fara da wasan da Dan Iyamura daga Guramada ya yi nasara a kan Kwaro daga bangaren Jamus.

Sauran da suka kai zagayen gaba a wasannin farko sun hada da Dan dabar Autan Dan Bunza daga Arewa da ya yi nasara a kan Musa Shagon Ebola daga Kudu.

Shi kuwa Sha’aban daga Kudu buge Bahagon Mancha daga Arewa ya yi a turmin farko, yayin da Shagon Bahagon Mancha daga Jamus ya buge Shagon Garkuwa daga Guramada.

Damben Zazu daga Kudu da Abba Shagon Roget daga Arewa ya kwana bayan turmi daya da suka buga, ranar Aalhamis za su karasa turmi biyu.

An kuma yi waje da Lagada – Ana sa ran bayar da ladan naira miliyan biyu ga wanda ya yi nasara.

Leave a comment