An dakatar da Barbosa na Brazil shekara biyu

An dakatar da dan kwallon tawagar Brazil da Flamengo, Gabriel Barbosa shekara biyu, bayan da aka same shi da laifin shirin shan abubun kara kuzarin wasa.

Wasu labarai daga jaridun cikin gida sun ce dan kwallon, wanda aka fi sani da suna Gabrigol ya kasa samar da yanayin da za a auna shi tun kafin ya buga tamaula a ranar.

Barbosa, wanda ya buga was Brazil wasa 18 ya musanta zargin da ake masa..

Barbosa, yana cikin tawagar Brazil da ta lashe lambar yabo ta zinare a Rio Olympics a 2016, yana da damar daukaka kara a kotun sauraren daukaka kara ta duniya.

Hukuncin shekara biyun ya fara daga ranar da aka tuhumi dan kwallon daga ranar 8 ga watan Afirilun 2023.

Za a fara kakar tamaula ta bana daga 14 ga watan Afirilu zuwa 8 ga watan Disamba, kenan Barbosa ba zai yi dukkan kakar bana, amma za a fara kakar 2025 da shi kenan.

Barbosa ya fara buga wa Brazil tamaula a karawar da ta dokePanama 2-0 a wasan sada zumunta a cikin watan Mayun 2016, wanda ya ci mata kwallo biyar.

Leave a comment