An dage wasan Bayern Munich da Berling

An soke wasan Bayern Munich da ya kamata ta buga da Union Berling ranar Asabar a Bundesliga.

Hakan ya biyo bayan rashin kyaun yanayi, bayan da dusar kankara ta yi ta zuba.

Bayern Munich ta ce saboda hadarin da yake ciki ya zama wajibi a dage karawar, za kuma a sanar da wata ranar buga fafatawar.

Za a iya buga wasan a filin Allianz Arena, amma yanayi na cuskoson abun hawa, yana daga cikin dalilin da aka dage wasan.

Haka kuma idan kankara ta taru da yawa a kan rufin filin zai iya zama hadari ga ‘yan kallo.

Sakamakon zubar dusar kankarar ba za ta bar wasu jami’ai da ‘yan kallo su je sitadiya ba.

Duk da cewar ana iya dumama filin wasa na Bayern Munich koda sanyi ya yi sanyi, matsalar lafiyar baki ake ji, wadanda za su je filin daga wuri mai nisa.

Ana kuma samun cuskoson abin sufiri da kuma a filin sauka da tashin jirgin sama.

Leave a comment