An daba wa mai goyon bayan PSG wuka

‘Yan Sanda a Italia sun sanar cewar an daba wa wani mai goyon bayan Paris St German wuka a shirin da kungiyar ke yi na karawa da AC Milan a Champions League ranar Talata.

Ba a bayyana sunan mutumin ba dan kasar Faransa, amma an ce ya ji mummunan rauni a Milan ranar Litinin, wanda aka garzaya da shi asibiti.

An ce mutumin mai shekara 34,, zai iya murmurrwa daga raunin da aka yi masa.

Wasu shaidu sun sanar da ‘yan sanda cewar kimanin magoya baya 50 na AC Milan da na PSG ne suka bai wa hammata iska a Arewacin birnin Novigli.

Bayan da aka kunna abubuwan tartsatsin wuta sai hayaki ya turnuke, inda aka ga wasu magoya baya dauke da sanduna sun kuma rufe fuskokinsu.

Wannan lamarin ya faru ne wata biyu da aka soka wa wani mai goyon bayan Newcastle United wuka a dai wurin da ya faru ranar Litinin a Champions League da Milan.

Millan za ta kara da PSG, wadda take jan ragamar rukunin shida da tazarar maki biyu,bayan da ta doke kungiyar Italiya 3-0 a karawar ta uku-uku a cikin rukuni.

Wasan na ranar Talata yana da mahimmamci ga kungiyoyin biyu, inda PSG ke fatan kai wa zagayen gaba, yayin da Milan ke fatan kara samun makin da za ta taka rawar gani a sauran wasannin.

Milan tana ta karshe a cikin rukuni na shida da maki biyu, wadda ta kasa cin koda kwallo ne a karawa ukun da ta buga.

Leave a comment