An ci tarar Fenerbahce an bai wa Galatasaray kwallo uku

An ci tarar Fenerbahce £98,450 an kuma bai wa Galatasaray cin kwallo uku da maki uku, bayan da kungiyar ta kauracewa wasan Turkish Super Cup ranar Lahadi.

Fenerbahce ta saka ‘yan wasanta ‘yan kasa da shekara 19, sannan ta fice daga fili a minti na uku.

Tun farko kungiyar ta bukaci a dage mata wasan sakamakon fafatawar quarter finals a Europa League kafin Alhamis da Olympiakos, amma ba a amince da rokon da ta yi ba.

Haka kuma Fenerbahce ba ta amince da alkalin wasan da aka nada zai busa karawar ta hamayya ba.

Kungiyar da take buga babbar gasar tamaula ta Turkiya ta bukaci a kawo wani raflin daga waje, amma hukumar kwallon kafar kasar ta ce ba ta amince ta yi hakan ba.

Ana take leda Galatasaray ta zura kwallo a raga a mintin farko ta hannun Mauro Icardi, daga nan kuma Fenerbahce ta umarci ‘yan wasa su fice daga filin.

Ita dai Fenerbahce ta zargi hukumar kwallon kafar Turkiya da yin rashin adalci, bayan da ta dakatar da ‘yan wasanta biyu daga buga karawa daya a lik, sakamakon fada da magoya bayan Trabzonspor, wadanda suka shiga fili makil ranar 17 ga watan Maris.

Haka kuma kungiyar ta yi yunkurin fita daga gasar Turkish Super Lig, amma sauran mambobin ba su amince da shirin ba.

Leave a comment