An ci tarar Barcelona kan halayyar wariya a wasa da PSG

An ci tarar Barcelona, sakamakon nuna halayyar wariya da magoya bayanta suka yi a wasan Champions League da Paris St Germain zagayen quarter final.

Haka kuma Uefa ta ce tana tuhumar Barcelona, dalilin da ya sa magoya bayanta suka kunna abubuwan tartsatsin wuta da ta kai an lalata wasu abubuwan a filin Parc des Princes.

An umarci kungiyar Spain ta biya tarar (£27,000).

Barca ta yi nasara a wasan farko a Paris da cin 3-2, amma aka doke ta 4-1 a wasa na biyu a Spain, hakan ya sa ta fita daga Champions League na bana.

Haka kuma Barcelona ba za ta sayar da tikiti ga magoya bayanta a wasan da za ta buga na gaba ba a gasar zakarun Turai da Uefa kan gudanar, wannan yana daga cikin karin hukuncin da aka yanke.

Haka kuma an bukaci Barcelona ta tuntubi Paris St Germain cikin kwana 30, domin ta biya dukkan asarar da aka yi a filin wasan.

PSG za ta buga karawar daf da karshe da Borussia Dortmund a Champions League.

Leave a comment