An ci Carrick a karon farko a riƙon ƙwarya a United

Newcastle United ta yi nasara kan Manchester United da cin 2-1 a wasan mako na 29 a Premier League da suka buga a St James Park ranar Laraba.

Mai masauƙin baƙi ta ci ƙwallayen ta hannun Gordon da kuma Osula, yayin da Casemiro ne ya ci wa United ƙwallo a fafatawar.

Sai dai kuma mai masaukin baƙi ta karasa fafatawar da ƴan ƙwallo a cikin fili, bayan da aka bai wa Ramsey jan kati tun a minti na 45.

Wannan shi ne karon farko da kociyan riƙon ƙwarya na United, Michael Carrick ya yi rashin nasara tun bayan da ya maye gurbin Ruben Amorim.

Kociyan tsohon ɗan wasan ƙungiyar Old Trafford ya ja ragamar wasa takwas da cin shida da canjaras ɗaya tun da ya fara aiki a cikin watan Janairu.

Da wannan sakamakon United ta ci gaba da zama a mataki na ukun teburin Premier League da maki 51, ita kuwa Newcastle mai maki 39 tana ta 12 a kasan teburin Premier League.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top