An bai wa PSG damar sayen Casemiro daga Man United

Wasu rahotanni na cewar an bai wa Paris St Germain damar sayen Casemiro daga Manchester United a watan Janairu.

Kan fara kakar 2022, Man United ta sayo dan kwallon tawagar Brazil kan £70m daga Real Madrid.

Casemiro ya taka rawa ganin a kakar farko a Old Trafford, mai kwallo bakwai a raga a wasa 51 da lashe League Cup.

To sai dai mai shekara 31 ya kasa nuna kansa a kakar 2023, wanda ya yi wasa 12, mai fama da jinya tun daga ranar 1 ga watan Nuwambar.

Man United, wadda ba ta kokari a bana ta yi ban kwana da Champions League, bayan da ta yi ta karshe a rukunin farko.

Kasa zuwa zagayen 16 zai hana Man United samun kudin da za ta sayo karin sabbin ‘yan wasa, kenan ya zama wajibi ta sayar da wasu da take da su.

Tun kan a fitar da Man United daga gasar zakarun Turai ta bana, wasu rahotanni na cewar Casemiro ya samu sabani da Erik ten Hag, zai bar Old Trafford.

Sai dai ba a tabbaci cewar ko lallai tsohon dan wasan Real Madrid zai bar Man United a Janairun 2024.

Casemiro yana da saukan kunshin kwantiragi da Man United da zai kare a karshen kakar 2026.

Leave a comment