Alexander Arnold da Alisson da Jota sun koma atisaye – Klopp

Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp ya ce Trent Alexander-Arnold da Alisson da Diago Jota sun koma atisaye bayan jinya, amma ba a fayyace ko za su fuskanci Atalanta ba.

Ranar Alhamis, Liverpool za ta karbi bakuncin Atalanta a wasan farko zagayen daf da na kusa da na karshe a Euruopa League da za su fafata a Anfield.

‘Yan wasan uku sun ji rauni a cikin Fabrairu, sun koma yin atisaye ranar Talata, bayan da suka murmure.

Alexander-Arnold ya ji rauni a cikin Janairu, wanda ya koma buga wa Liverpool wasa a karawa da Burnley a Premier League ranar 10 ga watan Fabrairu daga nan ya fama rauni ya kara komawa jinya.

Shi kuwa Alisson ya ji rauni a wajen atisaye daga nan mai tsaron raga, Caoimhin Kelleher ya maye gurbinsa, bayan da Liverpool ke sa ran lashe kofi uku a kakar nan.

Tuni ta dauki Carabao Cup a bana, sannan tana ta biyu a teburin Premier League da maki 71 iri daya da na Arsenal ta daya.

Haka kuma Liverpool ta ce dan kasar Spain, Stefan Bajcetic na daf da komawa taka leda, wanda ya yi fama da jinya, minti 72 kacal ya buga wa kungiyar Anfield a kakar nan.

Leave a comment