Alcaraz zai fuskanci Djokovic a ATP Finals.

Carlos Alcaraz zai fafata da Novak Djokovic a daf da karshe a ATP Finals da ake yi a Turin a Italiya.

Alcaraz ya yi nasarar doke Daniil Medvedev da cin 6-4, 6-4 ranar Juma’a ya kuma zama na daya a kan teburin mai launin ja..

Alcaraz ya kai matakin ne duk da baya kan ganiyarsa, sakamakon jinya da ya sha fama a baya, zai kuma fuskanci Djokovic ranar Asabar.

Djokovic, wand yake na daya a jerin wadanda ke kan gaba a kwallon tennis a duniya na fatan lashe kofi na bakwai a shekarar 2023.

Medvedev, wanda ya buga wasan karshe a ATP Finals a 2020 zai kara da Jannik Sinner, wanda ya zama dan Itliya na farko da ya kai daf da karshe a gasar ranar Alhamis,

Leave a comment