Al Hilal ta yi ta daya a rukuni a Asian Champions League

Mai rike da kofi hudu, Al Hilal ta kammala wasannin cikin rukuni a matakin farko a Asian Champions League.

Kungiyar Saudi Arabia ta doke Nassaji Mazandaran ta Iran da ci 2-1 ranar Litinin.

Al Hilal ta ja ragamar rukuni na hudu tun kan wasan ranar Litinin, hakan ya sa koci,Jorge Jesus ya ajiye Aleksandar Mitrovic da Sergej Milinkovic-Savic a benci.

Ruben Neves, wanda ya koma kungiyar a bana, baya cikin ‘yan wasan da suka buga karawar, yayin da Neymar ke jinya, wanda ya ji rauni cikin Oktoba, lokacin da yake buga wa Brazil wasa.

Minti hudu da take leda Al Hilal ta fara cin kwallo a wasan da aka yi a Prince Faisal bin Fahd Stadium.

Al Hilal, wadda ta sauya Golan Morocco, Yassine Bounou lokacin da aka je hutu, ta kara na biyu ne a minti na 54.

Leave a comment