Al Hilal ta hana Ronaldo daukar kofin Saudi

Ranar Asabar Al Hilal ta lashe kofin babbar gasar tamaula ta Saudi Arabia na hudu cikin kaka biyar, bayan da Cristiano Ronaldo bai samu daukar ko daya ba.

Al Hilal, wadda ta yi rashin neymar Junior a Oktoba, sakamakon raunin da ya ji, ta doke Al Hazm ta karshen teburi 4-1, kenan ta bai wa kungiyar Ronaldo, Al Nassr tazarar maki 12 kuma saura wasa uku a kammala kakar bana.

Al Hilal ta lashe kofin Saudi, bayan wasa 31 a lik ba tare da an doke ta ba, kuma wasa 34 a jere a dukkan karawa ba tare da rashin nasara ba.

Kungiyar da Jorge Jesus ke jan ragama tana da damar bugun kirji da cewar ita ce gwarzuwar gasar, bayan da Ronaldo ya koma tun Janairun bara da ya kara hada wasannin hamayya.

Fitattun ‘yan wasan dake buga gasar Saudi sun had da Neymar da Karim Benzema da Sadio Mane da N’Golo Kante da Riyad Mahrez da sauransu dake haskaka wasannin.

Manyan kungiyoyi hudu dake buga gasar Saudi da suka hada da Al Hilal da Al Nassr da Al Ittihad da kuma Al Ahli — dukka mallakin hannun jarin gwamnati ne.

Al Hilal za ta kara harzuka Ronaldo mai shekara 39 a lokacin da za su kara karawa a King Cup ranar 31 ga watan Mayu.

Leave a comment