Afcon 2025: Za a kara da Chad da Eswatini da Liberia da South Sudan a neman gurbi

Tawagar Chad da ta Eswatini da ta Liberia da kuma South Sudan sun kai matakin shiga wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Afirka ta 2025.

Kasashen sun yi nasarar wasannin da suka buga na neman cancantar shiga jadawalin buga neman gurbin shiga gasar Afcon 2025 da suka kara ranar Talata.

Tawagogin hudu za su cikin 44 nan gaba.domin kara raba wani jadawalin wasannin.

Sai dai hukumar kwallon kafa ta Afirka ba ta fayyace ranar yin jadawalin ba, da kuma ranar da za a fara gasar kofin Afirka a Morocco a 2025 ba.

To sai dai kuma gasar da FiFA za ta gudanar a Yuni zuwa Yuli na World Club Cup a 2025 zai ci karo da gasar Afcon.

Sakamakon wasannin da aka fafata don shiga Afcon 2025

Eswatini 2-2 Somalia (5-2 agg)

Mauritius 1-2 Chad (1-3 agg)

Liberia 0-0 Djibouti (2-0 agg)

South Sudan 0-0 Sao Tome and Principe (1-1 agg)

Leave a comment