Afcon 2024: Senegal ta bayyana ‘yan wasa 27

Aliou Cisse ya sanar da ‘yan wasan Senegal 27 da za su buga gasar kofin nahiyar Afrika, Afcon da za a yi a 2024.

Senegal, wadda ita take rike da kofin Afirka da ta dauka a 2022 a Cameroon ta gayyaci ‘yan wasan da ke taka leda a Turai da masu buga gasar Saudi Arabia.

Cikin masu taka leda a gasar Saudi Arabia sun hada da Sadio Mane da Edouard Mendy da kuma Kalidou Koulibaly.

Kociyan Senegal, mai shekara 47 na fatan lashe kofin na biyu a jere a karon farko, tun bayan bajintar Masar a 2010 da ta yi haka.

Senegal za ta buga wasanni a rukuni na uku da ya hada da Cameroon da Guinea da kuma Gambia.

Ivory Coast ce za ta karbi bakuncin gasar kofin nahiyar Afirka da za a fata daga 13 ga watan Janairu zuwa 11 ga watan Fabrairu.

‘Yan wasan Senegal 27 da za su buga Afcon 2024:

Masu tsare raga: Edouard Mendy (Al Ahli/KSA), Seny Dieng (Middlesbrough/ENG), Mory Diaw (Clermont/FRA)

Masu tsare baya: Kalidou Koulibaly (Al-Hilal/KSA), Abdou Diallo (Al-Arabi/QAT), Abdoulaye Seck (Maccabi Haifa/ISR), Abdoulaye Niakhate (Troyes/FRA), Moussa Niakhate (Nottingham Forest/ENG), Fode Ballo Toure (Fulham/ENG), Youssouf Sabaly (Real Betis/ESP), Ismail Jackobs (Monaco/FRA), Formose Mendy (Lorient/FRA)

Masu buga tsakiya: Nampalys Mendy (Lens/FRA), Idrissa Gueye (Everton/ENG), Pape Sarr (Tottenham/ENG), Pape Gueye (Marseille/FRA), Krepin Diatta (Monaco/FRA), Pathe Ciss (Rayo Vallecano/ESP), Cheikhou Kouyate (Nottingham Forest/ENG), Lamine Camara (Metz/FRA)

Masu cin kwallaye: Sadio Mane (Al Nassr/KSA), Habibou Diallo (Al Shabab), Iliman Ndiaye (Marseille/FRA), Ismaila Sarr (Marseille/FRA), Nicolas Jackson (Chelsea/ENG), Boulaye Dia (Salernitana/ITA), Abdallah Sima (Rangers/SCO)           

Leave a comment