Afcon 2024: Bafana Bafana ta bayyana ‘yan wasa 50

Tawagar kwallon kafa ta Afirka ta Kudu, Bafana Bafana ta bayyana ‘yan wasa 50 da za ta tantance wadanda za su buga mata gasar kofin Afirka.

Koci, Hugo Broos ne ya sanar da ‘yan wasan a shirin da kasar ke yi na zuwa Ivory Coast, domin gwada sa’a.

Cikin ‘yan wasa 50 da aka bayyana daga baya za su koma 23 da za su je gasar kofin Afirka da za a yi a 2024.

Za a buga gasar cin kofin Afirka karo na 34 a Ivory Coast da za a fara tsakanin 13 ga watan Janairu zuwa 11 ga watan Fabrairun 2024.

‘Yan wasan da aka gayyata za su je sansanin horo ranar 4 ga watan Janairu daga nan su koma Stellenbosch, inda za suyi atisayen kwana biyar.

Bafana Bafana za ta buga wasan sada zumunta da Lesotho a filin wasa na Lucas Moripe ba tare da ‘yan kallo ba a Atteridgeville daga nan ta je Côte d’Ivoire ranar 11 ga watan Janairun 2024.

Leave a comment