Kociyan tawagar Guinea, Kaba Diawara ya sanar da ‘yan wasa 25 da za su buga gasar kofin nahiyar Afirka da za a yi a Ivory Coast a 2024.
Wannnan shi ne karo na 13 da Guinea za ta kara a babbar gasar tamaula ta Afirka.
Tawagar da ake kira Syli National tana rukuni na uku da ya hada da Senegal da Cameroon da kuma Gambia.
Za a fara gasar cin kofin Afirka a Ivory Coast tsakanin 13 ga watan Janairu zuwa 14 ga watan Fabrairun 2024.
Wasannin da Guinea za ta buga a Ivory Coast a 2024.
Ranar 15 ga watan Janairu
- Cameroon da Guinea
Ranar 19 ga watan Janairu
- Guinea da Guinea
Ranar 23 ga watan Janairu
- Guinea da Senegal
Filin da rukuni na uku zai yi wasanninsa:
Charles Konan Banny Stadium, Yamoussoukro
‘Yan wasa 25 da za su buga wa Guinea Afcon 2023:
Wasu tsare raga:
- Aly Keita
- Moussa Camara
- Ibrahim Koné
Wasu tsare baya:
- Antoine Conte
- Ibrahima Diakite
- Issiagha Sylla
- Sékou Oumar Sylla
- Mouctar Diakhaby
- Julien Janvier
- Saidou Sow
- Mohamed Aly Camara
Masu buga tsakiya
- Amadou Diawara
- Seydouba Cisse
- Aguibou Camara
- Naby Keita
- Aboudoulaye Toure
- Mory Konate
- Moriba Kourouma
- Karim Cisse
Masu cin kwallaye
- Francois Kamano
- Morgan Guilavogui
- Serhou Guirassy
- Mohamed Bayo
- Jose Martinez Kante
- Facinet Conte