Afcon 2023: Mun dauki mataki kada a samu matsala irin ta Kamaru

Shirye-Shirye sun yi nisa da Ivory Coast ke shirin karbar bakuncin gasar kofin Afirka a 2024.

Hakan ne ya sa masu shirya wasannin ke fatan abinda ya faru a Kamaru a 2021 kada a maimaita shi a Ivory Coast.

Karo na biyu da Ivory Coast za ta karbi bakuncin wasannin, duk da cewar tana sawun gaba a taka leda a Afirka.

Ta fara gudanar da gasar a 1984 a lokacin da tawaga takwas, wannan karon da kasashe 24 za su kece raini a tsakaninsu.

Za a fara wasannin daga 13 ga watan Janairu zuwa 11 ga watan Fabrairu, Senegal ce mai rike da kofin da ta doke Masar a Kamaru ta lashe a karon farko a tarihi.

Tun farko an tsara buga wasannin cikin watan Yuni zuwa Yulin 2023, sai dai lokacin damuna ne a kasar, hakan ya sa hukumar kwallon kafar Afirka ta mayar da wasannin daga Janairu zuwa Fabrairu.

Ivory Coast ta tanadi tsaro daga cikin gida da makwabta, musammam Mali da Burkina Faso, inda ake fama da ‘yan tawaye, tana kuma yiwa jami’anta horo kan magance turmutsits.

A wasan da aka yi tsakanin Kamaru da Comoros aka ci karo da turmutsitsi da mutun takwas suka mutu da dama suka ji rauni wajen kokarin shiga kallon wasan.

Kenan Ivory Coast ta tanadi sojoji da ‘yan siyasa 17,000 da kuma masu aikin sa kai 2,500.

Leave a comment