Afcon 2023: Morocco na fatan kawo karshen shekara 47 rabon ta da kofin

Kociyan tawagar kwallon kafar Morocco, Walid Regragui, ya bayyana ‘yan wasa 27 da za su buga wa kasar gasar cin kofin Afirka a 2024.

Shekara 47 kenan rabon Morocco ta dauki kofin nahiyar Afirka, amma ana saka ta cikin wadanda ake cewa za su iya lashe kofin bana, bayan da ta kai daf da karshe a gasar kofin duniya a Qatar a 2022.

Tun bayan da Morocco ta dauki kofin a 1976, sau daya ta kai wasan karshe a 2004, wadda ta yi rashin nasara a hannun Tunisia.

A gasar da Cameroon ta gudanar a 2022, Masar ce ta fitar da Morocco a zagayen daf da na kusa da na karshe.

Regragui ya gayyaci ‘yan wasa da yawa daga cikin wadanda suka taka rawar gani a Qatar, wadanda suka ci Belgium da Spain da Portugal kafin rashin nasara a hanun France da ci 2-0 a daf da karshe.

Cikin ‘yan kwallon da ta gayyata har da mai taka leda a Paris Saint-Germain, Achraf Hakimi da na Sevilla, Youssef En-Nesyri da mai taka leda a Manchester United, Sofyan Amrabat.

Haka kuma kociyan ya kira sabbin jini da ya hada da mai wasa a PSV, Ismael Saibari da na Real Betis, Chadi Riad.

The Atlas Lions zai ta fuskanci Jamhuriyar Congo da Tanzania da kuma Zambia a gasar da za a fara daga 13 ga watan Janairu.

‘Yan wasan Morocco zuwa Afcon 2023:

Masu tsaron raga: Yassine Bounou (Al Hilal/KSA), Mounir El Kajoui (Al-Wehda/KSA), El Mehdi Benabid (AS FAR)

Masu tsaron baya: Achraf Hakimi (Paris Saint-Germain/FRA), Mohamed Chibi (Pyramids/EGY), Abdelkabir Abqar (Deportivo Alaves/ESP), Romain Saiss (Al-Shabab/KSA), Nayef Aguerd (West Ham/ENG), Yunis Abdelhamid (Rennes/FRA), Chadi Riad (Real Betis/ESP), Noussair Mazraoui (Bayern Munich/GER), Yahia Attiat Allah (Wydad Casablanca)

Masu buga tsakiya: Bilal El Khannouss (Genk/BEL), Azzeddine Ounahi (Marseille/FRA), Oussama El Azzouzi (Bologna/ITA), Sofyan Amrabat (Manchester United/ENG), Selim Amallah (Valencia/ESP), Amir Richardson (Reims/FRA), Hakim Ziyech (Galatasaray/TUR), Amine Harit (Marseille/FRA), Sofiane Boufal (Al-Rayyan)

Masu cin kwallo: Ismael Saibari (PSV Eindhoven/NED), Amine Adli (Bayer Leverkusen/GER), Ayoub El Kaabi (Olympiacos/GRE), Youssef En-Nesyri (Sevilla/ESP), Tarik Tissoudali (Gent/BEL), Abdessamad Ezzalzouli (Real Betis/ESP)

Leave a comment