AC Milan ta sanar Leao ya ji rauni ranar asabar

Dan kwallon tawagar Portugal, Rafael Leao ya ji rauni a wasan da AC Milan ta tashi 2-2 a gidan Lecce a Serie A ranar Asabar.

Leao, wanda aka sauya a karawar a Stadio Via del More bayan minti tara da take leda, Milan ba ta sanar da ranar da zai koma taka leda ba.

Wasu jaridun Italiya na cewa dan wasan mai shekara 24 zai yi jinyar mako biyu zuwa uku, kenan ba zai yiwa Portugal wasan neman gurbin shiga gasar kofin nahiyar Turai da za ta kara da Liechtenstein da kuma Iceland ba.

Leao ya ci kwallo hudu a kakar bana, har da wadda ya farke ranar Talata a Champions League da AC Milan ta doke Paris St Germain 2-1 a birnin Milan.

Leave a comment