Abinda ya kamata ku sani kan wasan Man United da Liverpool

Manchester United za ta karbi bakuncin Liverpool a Premier League ranar Lahadi a Old Trafford.

Liverpool za ta koma matakin farko a Premier League idan ta ci United, bayan da Arsenal ke jan ragama da maki 70 da tazarar maki daya tsakaninta da kungiyar Anfield.

Manchester United ta na ta biyar da maki 48 a wasa 30 da ta kara a babbar gasar tamaula ta bana ta England.

Wannan shi ne wasa na uku da za su fuskanci juna a bana, bayan da suka tashi ba ci a Premier a Anfield ranar 17 ga watan Disambar 2023.

Sai dai United ta yi waje da Liverpool a FA Cup na bana da cin 4-3 a Old Trafford ranar 17 ga watan Maris din 2024.

Bayanai kan lafiyar ‘yan wasa

Manchester United na jiran ji daga likitoco ko Casemiro da Jonny Evans da kuma Raphael Varane na cikin koshin lafiya, wadanda aka sauya a karawa da Chelsea.

Wadanda ke jinya a United sun hada da Victor Lindelof da Lisandro Martinez da kuma Luke Shaw

Wataru Endo na Liverpool ya murmure, wanda bai yi karawar da kungiyarsa ta doke Sheffield United ba, sakamakon raunin da ya ji a wasa da Brighton.

Wadanda ke jinya a Liverpool sun hada da Trent Alexander-Arnold da Alisson da kuma Diogo Jota.

Bayanai da ya shafi karawa a tsakaninsu

Wasa daya Manchester United ta yi nasara daga 11 baya da ta fuskanci Liverpool a Premier da yin canjaras hudu da rashin nasara shida.

Watakila United ta doke Liverpool wasa biyu a jere a Old Traford a karon farko tun bayan Satumbar 2015.

Wasan da United ta fitar da Liverpool a FA Cup shi ne nasara na biyar daga fafatawa 20 da Jurgen Klopp kociyan kungiyar Anfield.

An raba jan kati 18 a wasa tsakanin Manchester United da Liverpool a Premier League, karawar Everton da Liverpool ce kan gaba da aka bayar da jan kati 23.

Kungiyar Manchester United

Manchester United ta yi rashin nasara 17 daga 42 a dukkan karawa a kakar nan, wadda ta yi nasara 21 da canjaras hudu, an taba doke United wasa 19 a kakar 1977/78.

United ta yi kan-kan-kan da tarihin rashin nasara 12 a Premier League a kaka daya kamar yadda ta yi a 2013/14 da wanda ta yi a 2021/22, an kuma kori kociyan da suka yi wannan rashin kwazon a lokacin.

A karkashin Erik Ten Hag, United ta yi nasara hudu daga wasa biyar a gida da kungiyar da take hudun farko a makon da ta fuskance ta, har da cin Aston Villa 3-2 cikin Disambar 2023.

Kungiyar Liverpool

Liverpool ta ci wasa 16 da cin kwallo 59 a dukkan fafatawa a 2024, fiye da manyan kungiyoyin dake buga gasar lik biyar a Turai.

Kungiyar da Jurgen Klopp ke jan ragama ta samu maki 26 daga saura minti 15 a tashi daga wasa.

Ta kuma hada maki 26 daga karawar da ko dai a fara zura mata kwallo daga baya ta zare a tashi canjaras ko kuma ta samu maki uku.

Watakila Mohamed Salah ya zama na farko da zai ci United karo na hudu a jere a Premier League a Old Trafford.

Salah ya ci United kwallo 13 daga wasa 14 har da takwas da ya zura a raga a karawa biyar baya a Old Trafford a dukkan fafatawa.

Salah yana kan-kan-kan a tarihin cin United kwallo 10 a Premier League kamar yadda Alan Shearer keda tarihin.

Leave a comment