Abinda ya kamata ku sani kan wasan Liverpool da Atalanta

Liverpool za ta karbi bakuncin Atalanta a wasan farko a Europa League zagayen quarter finals da za su kara ranar Alhamis a Anfield.

Wannan shi ne wasa na uku da za su fuskanci juna a tsakaninsu, bayan da suka kara sau biyu a Champions League a kakar 2020/21.

Liverpool ce ta fara zuwa Italy ta ci 5-0 ranar Talata 3 ga watan Nuwambar 2020, amma kuma Atalanta ta yi nasara a wasa na biyu a Anfield da cin 2-0 ranar 25 ga watan Nuwambar 2020.

Liverpool, wadda tuni ta lashe Carabao Cup na fatan cin uku a bana har da na Premier League da take ta biyun teburi da maki 71 iri daya da na Arsenal ta daya.

Tuni dai FA Cup ya sullubemata a kakar nan, bayan da ta yi rashin nasara a hannun Manchester United da cin 4-3.

Liverpool na fatan daukar kofi da yawa a bana domin taya murna ga Jurgen Klopp, wanda ya sanar zai ajiye aikin a karshen kakar nan.

Tuni kuma kociyan ya sanar ranar Talata cewa Trent Alexander Arnold da Alisson da kuma Diago Jota sun koma atisaye, bayan jinya da suka yi fama tun daga Fabrairu.

Atalanta tana ta shidan teburin Serie A da maki 50, bayan da ta yi karawa 3o da kwantai daya.

Wasannin da za a buga ranar Alhamis a Europa League:

  • AC Milan da Roma
  • Liverpool da Atalanta
  • Bayer Leverkusen da West Ham United
  • Benfica da Olympique de Marseille

Leave a comment