Abinda ya kamata ku sani kan wasan Arsenal da Bayern Munich

Arsenal da Bayern Munich za su buga wasan farko a Champions League zagayen quarter finals ranar Talata a Emirates.

Wannan shi ne karo na 22 da Bayern Munich za ta buga zagayen daf da na kusa da na karshe a Champions League, wadda za ta kai ziyara England.

Wasa na 13 da za su kece raini a tsakaninsu, inda Bayern ta ci wasa bakwai, Arsenal ta yi nasara uku da canjaras biyu.

A wasa hudu baya a zagayen ziri daya kwale, Bayern ta yi nasara a kan Arsenal, wadda Gunners ba ta yi nasara a kanta a irin wannan matakin a gidan Arsenal.

Sau hudu Bayern Munich tana kai wa zagayen gaba a kan Arsenal a Champions League, yayin da kungiyar Germany ta yi nasara a karawa uku baya da cin 5-1 a kowanne.

Arsenal tana matakin farko a kan teburin Premier League da maki 71, iri daya da na Liverpool ta biyu da kuma Manchester City ta uku mai maki 70.

Gunners ba ta taba lashe Champions League ba a tarihi, wadda ke fatan dauka a karon farko a bana tare da Premier League, wanda rabon ta da shi kaka 20.

Bayern Munich tana da Champions League shida, wadda take ta biyu a teburin Bundesliga da tazarar maki 16 tsakaninta da Bayern Leverkusen mai jan ragama.

Leave a comment