Wai ina Ashiru Horo tsohon Sarkin damben gargajiya?

Ashiru Horo ɗaya ne daga tsaffin ƴan damben gargajiya da ya ya jarumta a faɗin Nigeria da za a daɗe ba a manta da shi ba.

Ya fara wasan tun daga matashi, ya kuma fara da bin Ali Zuma ɓangaren Guramaɗa daga baya ya koma Jamus.

Ya kuma buga damben a filaye da yawa a faɗin Naigeria ya kuma samu alheri, kuma sunasa ya ratsa ko ina a fannin damne.

Mutum ne da baya tsoro kuma yana bayar da nishadi ko a fili koda an gama dambe ya kuma iya mu’amala da magoya baya da makada da masu gidan dambe da ƴan kallo, amma wani lokacin kan nuna ɓacin ransa.

Yanzu dai ya daɗe da yin ritaya, sai dai iyayen gida da suke tunawa da shi da kuma wasu masu gidajen dambe

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top