Wa ya kai dambe kololuwa tsakanin Ali Zuma da Danliti?

Ali Zuma da Mamman Bashar Danliti suna daga cikin waɗanda suka farfaɗo da wasannin damben gargajiya a faɗin Nigeria.

Shi dai Ali Zuma yana gudanar da wasanninsa a DeiDei da ke Abuja, shi kuwa Danliti yan gudanar da sana’ar a filin wasa na Ao Bayero Square a jihar Kano, Nigeria.

Kenan sun yi nisa a tsakaninsu, amma kowacce rana suna shirya dambe da yawa da yake jan hankalin ƴan kallo.

Sai dai shi Ali Zuma ya fi samun cikar ƴan kallo a karshen mako, sakamakon mazauna abuja ma’aikata ne, sun fi samun hutu ranakun karshen mako.

Shi kuwa Danliti na samun ƴan kallo makil a kowacce rana har da karshen mako, saboda yawancin ƴan kallo ƴan kasuwa ne da zarar yamma ta yi sai a rufe kasuwance a je gidan dambe.

Tskanin Ali Zuma da Danliti, kowanne kan haɗa babban wasa da bayar da makudan kudi, amma an fi yawan yin gasa a filin wasa na Ado Bayero Square a jihar Kano.

A duk shekara Danliti kan sa damben motar Gwamnan Kano da damben Saraukar Sarkin Kano, ana kuma sa gasar matasa da ta babur ko dabba da sauransu.

Shi kuwa Ali Zuma kan sa damben naira dubu ɗari biyar 500,000 a wasa ɗaya, ya kan kuma bai wa magoya baya su zaɓi damben da suke sha’awar gani, domin a sa musu maƙudan kudi.

Dukkansu sun bayar da gudunmuwar da damben gargajiya ya farfaɗo da ta kai duk duniya ana sa’awar ganin wasannin na Bahaushe.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top