Gasar Premier ta Nigeria ta bana NPFL ta yi nisa ta shiga matakin gangara, bayan da za a fara wasannin mako na 29 a karshen mako.
Hakan ya sa muka yi duba na tsakani kan manyan abubuwa biyar da suka fi ɗaukar hankali a kakar bana.
1️⃣ Zafin Gasa a Teburin Gasar
Nigeria Premier Football League
A kakar bana an ga yadda ake kalubalantar juna tsakanin ƙungiyoyi, musamman a saman tebur da masu kokarin kada su faɗi daga gasar. Bambancin maki tsakanin kungiyoyin gaba ba shi da yawa, wanda ya sa kowane wasa yake da muhimmanci.
Daga tsakanin ƴan biyar ɗin farko tazarar maki tsakanin ƙungiyoyi bai kai uku ba, misali Rivers ce ta ɗaya da maki 49 da tazarar maki biyu tsakaninta da Rangers, haka kuma Ikorodu ce ta uku da tazarar maki biyu tsakani da Rangers, Nasarawa United ce ta huɗu da tazarar maki ɗaya tsakaninta da Ikorodu, sannan Abia Warriors ta biyar ɗin teburi da maki 43 da tazarar ɗaya tsakani da Nasarawa United.
2️⃣ Ana Ta Faɗi Tashi Tsakanin Ƙungiyoyin kasan teburi
A karshen teburin NPFL na bana Kun Khalifat ce ta karshe da maki 29 iri ɗaya da na Kwara United, Sai Remo Stars maki 30 ne da ita da kuma Kano Pillars ta 17 mai maki 32 iri ɗaya da na Wikki Tourist ta 16 a kasan teburi.
Haka kuma sauran da ke biye tazarar maki baya wuce ɗaya ko biyu, hakan na nufin idan kaci wasa za ta iya tsintar kanka ka kara yin sama, da zarar ka yi rashin nasata ka kara nutsawa kasan teburin NPFL.
3️⃣ Fitowar Matasa ‘Yan Wasa
A bana an ga matasa ƴan wasa da dama suna haskakawa a ƙungiyoyi daban-daban. Wannan na nuna cewa ƙungiyoyin NPFL na bai wa matasa dama su nuna basirarsu.
4️⃣ Karin Magoya Baya a Filayen Wasanni
A wasu birane kamar Kano, Aba da Ibadan an ga ƙaruwar magoya baya da ke zuwa kallon wasa a filin. Wannan zai kara armashi da sha’awar gasar.
5️⃣ Wasanni Masu Kayatarwa
A kakar bana an ga wasanni da aka sharara kwallaye da kuma fafatawa ta hamayya, wanda ya sa NPFK ta fi jan hankali ga masu sha’awar kwallon kafa a Najeriya.
✅ A takaice:
NPFL ta bana ta kasance mai daukar hankali saboda zafin gasa, dawowar manyan kungiyoyi, fitowar matasa, da kuma karuwar magoya baya a filayen wasa. ⚽
