Me zai faru a wasan mako na 29 a gasar Premier ta NPFL?

A mako na 29 a Nigeria Premier Football League, za a yi karawa 10 daga ciki akwai manyan wasannin da za su ja hankli daga ciki har da na hamayya da za a yi a jihar Kano, Nigeria.

Kano Pillars vs Barau FC – filin wasa na Sani Abacha Stadium, Kano

  • Kano Pillars ce za ta kasance mai masaukin baƙi, wadda ake kira sai masu gida da take fatan ɗaukar fansa a wasan na hamayya.
  • Barau FC na neman maki domin kara yin nisa a kan teburin NPFL, da yake wannan shi ne karon farko da take buga wasannin. .
  • Bisa tarihin wasan da suka buga a kakar nan, Barau FC ce ta yi nasara 2-1 a cikin watan Oktoba ba tare da ƴan kallo ba, saboda a lokacin an hukunta Pillars, saboda matsala da ta samu a gida a wasa da 3SC.

Matsayin Ƙungiyoyi a Teburin Gasar:

  • Kano Pillars: tana ta 17 da Maki 32 daga wasa 28 da yin nasara 10 da canjaras biyar aka doke ta 13.
  • Barau FC: tana mataki na da Maki 37 daga wasa 28 da cin tara da canjaras 10 aka doke ta tara daga

Hasashen:

  • Fafatawar za ta ja hankali ganin ta hamayya ce, domin suna buga wasanninsu a Sani Abacha Stadium.
  • Kano Pillars na bukatr maki uku a wasan ganin da ta ke kasan teburi, domin kada ta ci gaba da fuskantar haɗarin barin NPFL a bana..
  • Barau FC ta raba teburin gida biyu ba ta da fargabar faɗawa cikin ƴan karshen teburi, kenan za ta yi fatan ganin ta kara sama a teburin gasar.

Filin wasa na Sani Abach da ke kofar mata zai ɗauki ƴan kallo ganin wasa na biyu da za su buga a NPFL, sannan magoya baya za su so ganin rawa da bajintar da ƙungiyars za ta yi musu.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top