Dele ya koma atisaye a Tottenham bayan barin Como

Tsohon ɗan wasan Tottenham, Dele ya koma ƙungiyar da ci gaba da yin atisaye, bayan da yarjejeniyarsa ta kare a Como mai buga Serie A.

Ɗan wasan ya kwashe shekara bakwai a ƙungiyar ta arewacin London, kafin ya bar ta a shekarar 2022. Yanzu an ba shi damar shiga cibiyar motsa jiki ta Tottenham wato Hotspur Way domin yin atisaye shi kadai.

Dele ya sha fama da matsalolin rashin ƙoshin lafiya da raunuka a ƴan shekarun baya, kuma tun bayan da ya bar Tottenham zuwa Italiya ta Como a watan Satumba, yanzu bai da wata ƙungiya.

Ɗan ƙwallon mai shekara 29 ya buga wasa daya kacal a kakar 2024/25 tare da Como.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top