Burnley ta yi ban kwana da Premier League

Burnley ta fice daga Premier League ta bana, bayan da Tottenham ta doke ta 2-1 ranar Asabar a wasan mako na 37.

Kungiyar da Vincent Kompany ke jan ragama ta ui fatan cin Tottenham, domin ta samu damar ci gaba da zama a babbar gasar tamaula ta Ingila a badi a wasan karshe ranar Lahadi.

Ranar 19 ga watan Mayu za a gama wasannin kakan bana, inda Burnley za ta kece raini da Nottingham Forest.

Burnley ce ta fara cin kwallo ta hannun Jacob Bruun Larsen daga baya Tottenham ta farke ta hanun Pedro Porro, sannan Micky van de Ven ya kara na biyu.

Burnley tana ta 19 a kasan teburin Premier da tazarar maki biyar tsakani da Nottingham Forest ta hudun karshe, kuma saura wasa daya ya rage a kammala kakar bana.

Burnley ta bi sawun Sheffield United zuwa Championship a badi, wadanda suka hau kakar bana.

Yanzu kungiya daya ake bukata ranar karshe da za a fayyace ukun da za su koma buga Championship a badi.

Leave a comment