Silva ya amince da kwantiragin kaka biyu da Fluminense

Thiago Silva ya amince zai koma tsohuwar kungiyarsa Fluminense, ya amince da kwantiragin kaka biyu da zarar yarjejeniyarsa ta kare a Chelsea a karshen bana.

Mai shekara 39 zai koma Brazil da taka leda, kungiyar da ya buga wa tamaula tsakanin 2006 zuwa 2008, wanda Chelsea ta amince ya koma kungiyar tun kafin kwantiragin sa ya kare a ranar 1 ga watan Yuli.

Zai bar Stamford Brige, bayan shekara hudu a London, kungiyar da ya yi wa wasa 150, tun bayan da ya koma kungiyar daga Paris St Germain, wanda ya lashe Champions League a 2021.

Magoya bayan Chelsea sun yi dan kwallon tawagar Brazil tafi, lokacin da za a sauya shi a wasan da Chelsea ta caskara West Ham 5-0, sakamakon rawar da ya taka.

Ana sa ran zai buga wasan karshe a Stamford Bridge a lokacin da Chelsea za ta kara da Bournemouth a Premier League.

Chelsea, wadda Mauricio Pochettino ke jan ragama na fatan neman gurbin shiga gasar zakarun Turai a badi, za ta fuskanci Nottingham Forest da Brighton.

Newcastle tana mataki na shida a teburin Premier League, sannan Chelsea ta bakwai mai maki 54, iri daya da na Manchester United ta takwas.

Leave a comment