Bayern leverkusen ta buga wasa na 46 a bana ba tare da an doke ta ba, bayan da ta tashi 2-2 da Stuttgart a Bundesliga ranar Asabar.
Wannan shi ne wasan farko da ta buga a gida a Bay Arena a matakin mai rike da kofi Bundesliga da ta dauka na farko a tarihi, bayan shekara 120 da kafa kungiyar.
Tun farko Sturttgart ta fara cin kwallaye biyu ta hannun Chris Fuhrich da kuma Deniz Undav, bayan da suka koma zagaye na biyu a wasan.
Daga baya ne Leverkusen ta zare daya ta hannun Amine Adli, sannan Robert Andrich ya farke na biyu daf da za a tashi daga karawar.
Leverkusen wadda ta lashe Bundesliga tun kan kammala kakar bana ta ci wasa 38 da canjaras takwas a dukkan karawar da take yi a bana.
Cikin wasannin da take fafatawa sun hada da Bundesliga da German Cup da kuma Europa League.
Kungiyar dake fatan lashe kofi uku a bana ta fara daukar Bundesliga daga hannun Bayern Munich, wadda ta lashe 11 a jere.
Haka kuma Bayern Leverkusen za ta buga daf da karshe gida da waje a Europa League da Roma, sannan za ta kara a wasan karshe a German Cup da Kaiserslautern.
Wasannin da ke gaban Bayern Leverkusen da suka raga a bana:
Europa League Alhamis 2 ga watan Mayu
- Roma da Bayern Leverkusen
Bundesliga Lahadi 5 ga watan Mayu
- Frankfurt da Bayern Leverkusen
Europa League Alhamis 9 ga watan Mayu
- Bayern Leverkusen da Roma
Bundesliga Lahadi 12 ga watan Mayu
- Bochum da Bayern Leverkusen
Bundesliga Asabar 18 ga watan Mayu
- Bayern Leverkusen da Augsburg
German Cup Asabar 25 ga watan Mayu
- Kaiserslautern da Bayern Leverkusen