Ko Barcelona za ta doke Valencia kuwa a La Liga?

Barcelona za ta karbi bakuncin Valencia a wasan hamayya a La Liga ranar Litinin.

Barcelona za ta kara da Valencia wasa na biyu a bana a La Liga ranar Litinin 23 ga watan Afirilu.

Kungiyoyin sun tashi 1-1 a wasan farko a kakar bana ranar 6 ga watan Disamba da valencia ta karbi Barca.

Joao Felix ne ya fara ci wa Barcelona kwallon daga baya Hugo Guillamon ya farkewa Valencia.

Barcelona tana ta biyu a teburin La Liga da tazarar maki 14 tsakani da Real Madrid mai shirin lashe kofi na 36 jimilla a kakar nan.

Ita kuwa Valencia tana ta takwas din teburin La Liga da maki 47, bayan wasa 32.

Tuni dai Barcelona mai La Liga na bara ta sanar cewar kociyanta Xavi zai ci gaba da horar da shekara daya, kenan zuwa karshen kakar 2027

Ranar Juma’a Real Madrid ta je ta doke Real Sociedad a wasan mako na 33 a La Liga.

Tuni Real Madrid ke shirin fuskantar Bayern Munich a Champions League gida da waje zagayen daf da karshe.

Real Madrid ce ta fitar da Manchester City mai rike da kofin bara daga wasanni bana a Etihad a bugun fenariti bayan da suka tashi 1-1.

Leave a comment