‘Yan Real da za su je Real Sociedad buga La Liga

Real Madrid za ta je gidan Real Sociedad domin buga wasan mako na 33 a La Liga ranar Juma’a.

Real Madrid wadda ta ziyarci Reale Arena tana ta daya a kan teburi da mki 81 da tazarar 11 tsakaninta da Barcelona ta biyu.

Ita kuwa Sociedad mai fatan neman gurbin shiga gasar zakarun Turai ta badi tana ta shidan teburi da maki 51.

Kungiyoyin biyu sun kara ranar 17 ga watan Satumbar 2023, inda Real Madrid ta yi nasara da cin 2-1 a Santiago Bernabeu.

Sociedad ce ta fara cin kwallo ta hannun Ander Barrenetxea a minti na biyar da fara tamaula, haka suka je hutu an zura kwallo daya a ragar Real Madrid.

Bayan da suka huta suka koma zagaye na biyu ne Real ta farke ta hannun Federico Valverde, sannan Joselu ya kara na biyu a minti na 60.

Real Madrid na daf da lashe La Liga na bana kuma na 36 jimilla, wadda za ta karbi kofin a hannun Barcelona mai rike da na bara.

Tuni koci, Carlo Ancelotti ya bayyana ‘yan wasan da Real Madrid ta je da su Sociedad.

‘Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Lunin, Kepa da Fran.

Masu tsaron baya: Carvajal, Militão, Nacho, Lucas Vázquez, Fran García da Rüdiger.

Masu buga tsakiya: Bellingham, Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni, Ceballos da Arda Güler.

Masu cin kwallaye: Vini Jr., Joselu da Brahim.

Leave a comment