Courtois na daf da komawa buga wa Real wasanni

Mai tsaron raga, Thibaut Cortois na daf da fara buga wa Real Madrid wasanni a lokacin da ake daf da karkare kakar tamaula ta bana.

Carlo Ancelotti ne ya sanar da hakan ranar Alhamis cewar golan tawagar Belgium ya warke daga jinyar da ya sha.

Sai dai Ancelotti ya ce ba zai yi gaggawar saka Courtois a wasa ba, wanda bai yi karawa ba a kakar nan, tun bayan raunin da ya ji cikin Agusta, sannan ya fama ciwon a cikin watan Maris.

Kenan Andriy Lunin ne zai tsare ragar Real Madrid ranar Juma’a a karawa da Real Sociedad a La Liga da kuma wasan farko a daf da karshe a Champions League a Bayern Munich daga nan sai ta yi amfani da Courtois.

Tun farko an dauka cewar raunin da Courtois ya je zai kawo koma baya ga Real Madrid a kakar nan, amma sai golan Ukraine, Luinin ya taka rawar da ake bukata, bayan da golan da ta dauka daga Chelsea, Kepa Arizabalaga ya gaza.

Lunin ne ya kai Real Madrid zagayen gaba a Champions League a bugun fenariti a gidan Manchester City, wanda ya buge biyu daga 4-3 da kungiyar Spain ta yi nasara, wadanda suka tashi 1-1 a Etihad.

Courtois mai shekara 31, ana sa ran zai koma kan ganiya da zarar ya fara wasa, inda Real Madtrid ke turbar lashe La Liga da kuma Champions League kawo yanzu.

Real ce ta daya a kan teburin La Liga da maki 81 da tazarar maki 11 tsakani da Barcelona ta biyu, wadda ta doke 3-2 a El Clasico ranar Lahadi.

Tuni dai Real Madrid na turbar daukar La Liga na 36, bayan da Barcelona keda rike da na bara.

To sai dai da kyar ne idan Jude Bellingham da Rodrygo za su buga wa Real wasan da za ta buga ranar Juma’a da Sociedad, sakamakon rashin lafiya, yayin da har yanzy Ferland Mendy ke jinya.

Leave a comment