Real Madrid na shirin fuskantar Real Sociedad a La liga

Real Madrid na shirye-shiryen fuskantar Real Sociedad a wasan mako na 33 a La Liga ranar Juma’a.

Kungiyar Santiago Bernabeu, wadda ke shirin lashe La Liga na 36, ita ce za ta je ta fuskanci Sociedad ranar Juma’a a filin Reale Arena.

Real Madrid ta ci 2-1 a wasan farko da suka buga a bana ranar 17 ga watan Satumbar 2023 a Santiago Bernabeu, inda Federico Velverde da Joselu suka ci mata kwallayen, Ander Barrenebea ya zare wa Sociedad daya.

Kungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama tana ta daya a kan teburin La Liga da maki 81 da tazarar maki 11 tsakani da Barcelona ta biyu, ita kwa Sociedad mai maki 51 tana ta shidan teburi.

Real Madrid ta fara atisaye a rufaffen daki, daga baya ta fito fili, inda ‘yan kwallo suka yi ta lailaya tamaula da rabawa a tsakaninsu.

Daga baya suka raba kwallon a tsakaninsu a dan karamin fili da suka raba biyu, yayin da Courtois da Alaba ke atisayen murmurewa daga jinya, yayin da Mendy ya motsa jiki shi kadai.

Real na shirin fustankar Bayern Munich a daf da karshe a Champions League gida da waje.

Leave a comment