UEFA ta bukaci a kara inganta hukuncin VAR

Hukumar kwallon kafa ta Turai, UEfA ta ce akwai bukatar hukuncin da ya kamata da yin keke da keke da ‘yan wasa da magoya baya da koci za suke amincewa da hukuncin VAR.

Ranar Litinin aka yanke wannan shawara tsakanin tsoffin ‘yan wasa da koci da suka yi taro a Nyon a Switzerland, kan korafi da ake ta samu kan hukuncin VAR.

An bayar da shawarar cewar VAR wata na’ura ce da ya kamata take taimakawa alkalan tamaula yanke hukunci, ba wai kawai za a ke yanke hukuncin barkatai ba.

UEFA ta fitar da wadan nan kalaman, sakamakon kura-kuren da VAR ta yi a Premier League.

Nottingham Forest ta bukaci a ba ta kalaman da aka yi tsakanin alkalin wasa da mai kula da VAR, bayan da ta yi korafin an hanata fenariti uku.

Sai dai hukumar gudanar da Premier ta ce bai kamata Forest ta kai batun kafar sada zumunta ba, inda batun ya koma na cece-kuce.

Haka itma Coventry City ta ci Manchester City kwallo, amma VAR ba ta karba ba, inda suka tashi 3-3 a FA Cup da United ta kai zagayen karshe ranar Lahadi.

Leave a comment