Tudun Wada United ta fitar da wadanda za su kara da Junior Danburan ranar Talata da yamma.
Kungiyoyin za su kara a wasa na uku a cikin rukuni a Nationwide League One a Daura jihar Katsina.
Tudun Wada United mai rike da kofin League two na bara ta yi nasara daya da canjaras daya daga wasa biyu cikin rukuni.
A ranar Asabar Tudun Wada United ta tashi 1-1 da Mumbayya FC, sannan ta doke Famours Spiders 3-1 ranar litinin.
Kenan tana da kwallo hudu an zura mata biyu a raga da maki hudu daga wasa biyu.
Tuni Anas kociyan Tudun Wada United ya bayyana ‘Yan wasan da za su fuskanci Junior Danburan, wadda a filinta ake yin wasannin NLO 2024 shiyyar Daura, Nigeria.
Za su kara ne da karfe hudu agogon Nigetia ranar Talata.
Jerin ‘Yan wasan Tudun Wada United:
1–Muwdda muhd
2–Abdullahi Abubakar
3–Dickson ricky
4–Safiyanu Abdullahi
5– Najibullah musa
6–Salisu idiris
7–Jerry Okon
8–Nasiru Abdullahi
9–salisu Abdullahi
10–Aminu muhammad
11–Rabiu Abdullahi
Masu jiran ko-ta-kwana
12.–Sulaiman Haruna
13–Rabiu sani umar
14–Abdurahaman m ismail
15–Nasiru Hamza
16– yusif muhammad
17–Musa Yahaya
18–Nazifi muhd
19–Usman Garba
20–Tahir Adam L
21–Abdullahi Y A
22–Rabilu Hamza
23–Abdullahi Rabiu