Bellingham ne na biyu a yawan cin kwallaye a La Liga

Ranar Lahadi Real Madrid ta doke Barcelona 3-2 a gasar La Liga karawar hamayya ta El Clasico a Santiago Bernabeu.

Bellingham ne ya ci wa Real kwallo na ukun da ya bai wa kungiyar maki ukun da take buga, wadda ta ci gaba da jan ragamar teburin La Liga.

Karon farko da dan wasan England ya zura kwallo a raga a wasan Real tun bayan fafatawa da aka doke Girona 4-0 ranar 10 ga watan Fabrairu, wanda ya zura biyu a ragar a karawar.

Bellingham wanda aka yi wa jan kati a wasa da Valecia ranar 12 ga watan Maris a wasan La Liga da suka tashi 2-2 ya ci wa England kwallo a wasan sada zumunta a Wembley da suka tashi 2–2 cikin watan Jiya.

Wasa na uku da Real ta ci Barcelona a kakar nan, bayan da ta yi nasara a kanta a La Liga da kuma a Spanish Super Cup a Saudi Arabia.

Bellingham, wanda ya buga wa Real wasa 26 a La Liga ya ci kwallo na 17 a bana a lik, shi ne kan gaba a cin kwallaye tsakanin ‘yan wasa kungiyar Santiago Bernabeu a kakar nan.

Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a La Liga

  • Artem Dovbyk Girona 18
  • Jude Bellingham Real Madrid 17
  • Ante Budimir Osasuna   16
  • Alexander Sorloth Villarreal 15
  • Borja Mayoral Getafe 15
  • Alvaro Morata Atletico Madrid 14
  • Vinicius Junior Real Madrid 13
  • Antoine Griezmann Atletico Madrid 13
  • Robert Lewandowski  Barcelona13
  • Gorka Guruzeta Athletic Bilbao 12
  • Hugo Duro Valencia 12

Leave a comment