Nagelsmann zai ci gaba da horar da Germany zuwa bayan 2026

Kocin tawagar Germany, Julian Nagelsmann ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da jan ragamar kasar zuwa bayan gasar kofin duniya da za a yi a 2026.

Nagelsmann, mai shekara 36, ya maye gurbin Hansi Flick cikin Satumbar 2023, kuma ya ci wasa uku daga shidan da ya ja ragama kawo yanzu.

Tun farko kunshin kwantiraginsa zai kare a karshen Yuli, bayan Germany ta gama gudanar da Euro 2024.

Har yanzu ba a fara wasannin neman shiga gasar kofin duniya ba a Turai, gasar da USA da Canada da kuma Mexico za su yi hadakar karbar bakunci a 2026.

Germany ta kasa haura zagayen ‘yan 16 a manyan gasa tun daga 2016, wadda aka yi waje da ita a karawar cikin rukuni a gasar kofin duniya a Russia da kuma Qatar, wadda ta kasa yin abin kirki a Euro 2020 a England.

Germany tana rukuni daya da Scotland da Hungary da kuma Switzerland a Euro 2024.

Tun farko an alakanta Nagelsmann da cewar zai sake karbar aikin horar da Bayern Munich a karshen kakar nan, domin maye gurbin Thomas Tuchel.

Germany ta yi nasarar cin France da Netherlands a wasan sada zumunta, za kuma ta fafata da Ukraine da Greece cikin Yuni a shirin da take na taka rawar gani a Euro 2024.

An yi waje da dukkan kungiyoyin Premier League daga Champions da Europa League na bana a zagayen quarter finals Latsa nan domin ci gaba da karatu

Leave a comment