Ancelotti ya ja ragamar wasa da yawa a La Liga kamar na Zidane

Ranar Asabar Real Madrid ta je ta doke Real Mallorca 1-0 a wasan mako na 31 a La Liga, kenan ta ci gaba da jan ragamar teburin babbar gasar tamaula ta Spain.

Real din ta ci kwallon ne minti uku da suka koma zagaye na biyu bayan hutu ta hannun dan wasan tawagar France, Aurelien Tchoumeni.

Wasa na 183 kenan da Carlo Ancelotti ya ja ragamar Real Madrid, wanda ya yi kan-kan-kan da yawan na Zinedine Zidane da ya horar da kungiyar Santiago Bernabeu.

Koci daya ne kan gaba a yawan jan ragamar Real Madrid wasa da yawa a La Liga shi ne Miguel Muñoz mai 424.

Bayan da Real ta ci Mallorca ranar Asabar ya zama Ancelotti ya yi nasara 131 a La Liga a kaka ta biyar da yake horar da kungiyar da canjaras 28 da rashin nasara 24.

Kociyan dan kasar Italy ya lashe La Liga a 2021/22, wanda ke rike da tarihin lashe babban kofin tamaula a Spain La Liga da Italy Serie A da Germany Bundesliga da England Premier Leage da kuma France Ligue 1.

Leave a comment