‘Yan Real Madrid da suka je gidan Mallorca buga La Liga

Real Mallorca za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan mako na 31 a La Liga ranar Asabar da za su fafata a filin wasa na Son Moix.

Sun kara ranar 3 ga watan Janairu a Santiago Bernabeu, inda Real Madrid ta ci 1-0 ta hannun Antonio Rudiger.

Mallorca mai maki 30 tana ta 15 a kasan teburin La Liga, bayan buga karawa30, ita kuwa Real Madrid, wadda take ta daya da maki 75 ta bai wa Barcelona ta biyu tazarar maki takwas.

Aa tsakiyar mako Real Madrid ta tashi 3-3 da Manchester City a zagayen daf da na kusa da na karshe a Champions League wasan farko a Spain.

Ranar 18 ga watan Afirilu Real Madrid za ta je Etihad, domin tantance wadda za ta kai zagayen daf da karshe a gasar zakarun Turai.

Ita kuwa Real Mallorca ta yi rashin nasara a wasan karshe a Copa del Rey a bugun fenariti a hannun Athletic Bilbao ranar Asabar.

‘Yan wasan Real Madrid:
Masu tsare raga: Lunin, Kepa da kuma Mario de Luis.
Masu tsare baya: Carvajal, Militão, Nacho, Lucas Vázquez, Fran García, Rüdiger da kuma Mendy.
Masu buga tsakiya: Bellingham, Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni, Ceballos da kuma Arda Güler.
Masu cin kwallo: Vini Jr., Rodrygo, Joselu da kuma Brahim.

Leave a comment