An kori mai sharhin tamaula bayan kalamai kan Yamal

An kori wani mai sharhin tamaul a talabijin a Spain, bayan wani kalamai da ya yi mai sarkakiya kan dan wasan Barcelona, Lamine Yamal.

Ya kuma yi kalaman ne tun kan wasan da Barcelona ta je ta ci Paris St German 3-2 ranar Laraba a wasan farko a Champions League zangon daf da na kusa da na karshe.

German Burgos, wanda ke aiki da Movistar, ya yi kalaman ne a lokacin da aka nuna Yamal yana wasa da tamaula.

Ana zargin Burgos da cewar ”Da kwallon ba ta karbe shi ba, da ya kasance a kan titi wajen da fitilu ke bayar da hannu.”

Barcelona da PSG sunki yin hira da Movistar, bayan da suka tashi daga gasar zakarun Turai.

“Movistar Plus+ ta yi tir da lamarin ta kuma ce ba za ta bayar da dama ga duk wani mutun mai aiki tare da shi ya ci zarafin wani ko kalaman da ba su dace ba.

An fassara kalamn da ya yi da cewar yana kwatanta Yamal da matasa ke nuna fasaharsu ta wasa da tamaula a wajen da fitulu ke bayar da hannu.

Burgos ya nemi afuwa kan kalaman da ya yi.

An haifi Yamal, mai shekara 16 a Spain, wanda iyayensa daga Morocco da kuma Equatorial Guinea.

Burgos, 54, ya yiwa Argentina wasa 35 lokacin da yake taka leda da yin kaka shida a Spain a Mallorca da kuma Atletico Madrid.

Leave a comment