Tawagar kwallon kafa ta mata ta Nigeria ta samu gurbin shiga gasar Olympic, bayan da ta je ta tashi ba ci a South Africa ranar Talata.
Karon farko da Super Falcons za ta buga tamaula a Olympic tun bayan shekara 16, inda birnin Paris a France ne zai karbi bakuncin wasannin bana.
Ranar Juma’a suka buga wasan farko a Abuja, Nigetia, inda Super Falcons ta yi nasarar cin Banyana Banyana 1-0, kenan ta kai gasar Olympic da cin kwallo 1-0 gida da waje.
Kenan har yanzu Banyana Banyana ta kasa ganin ranar da za ta doke Super Falcons a South Africa a fannin kwallon kafar mata.
Cikin wasa 24 baya da suka kara an buga bakwai a South Africa, inda Super Falcons ta lashe 15 daga ciki da canjaras biyar, inda ta yi rashin nasara hudu.
A karawa bakwai baya a South Africa, Nigeria ta yi nasara biyar da canjaras biyu.